✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da malamarsu

Mahara sun kashe wani mutum sannan suka yi awon gaba da dalibai bakwai da malamarsu a jihar Kaduna. Lamarin na safiyar Litinin a Prince Academy…

Mahara sun kashe wani mutum sannan suka yi awon gaba da dalibai bakwai da malamarsu a jihar Kaduna.

Lamarin na safiyar Litinin a Prince Academy da ke garin Damba-Kasaya na Karamar Hukumar Chikun, ya jefa mazauna cikin tashin hankali.

’Yan bindigar sun shiga makarantar ce a daidai lokacin da yaran suke shirye-shiryen rubuta jarabawar karshe ta aji uku na sakandire (JSCE).

“Sun shigo suna harbe-harbe kafin suka shiga makarantar da suka dauke daliban da ake yi wa karatun don fuskantar jarabawa kammala aji uku.

“Yaran da aka sace ba su wuce shekaru 12 da kin ba. Mun tabbatar da sun dauke yara mata da maza bakwai, tare da wata malama. Sun kuma tafi da wani manomi da suka samu gonarsa”, inji wani mazaunin garin.

Ya ce ’yan bindigar “Sun kuma kashe wani makwabcin makarantar wanda ya mutu ya bar matarsa da jariri”.

Ya ce mutanen gari sun bi sawun barayin, wanda hakan ya sa suka saki wasu mutanen da suka sace amma daga wani gari.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin.

Gwamnatin Tarayya ta ba da damar dalibai su rubuta jarabawar kamala firamare da karama da kuma babbar sakandare bayan annobar coronavirus ta sa an rufe makarantu.