’Yan bindiga sun sace daliba a cikin dare a wata makaranta ke cikin garin Kaduna.
Majiyoyi a Kwalejin ta Horon Samar da Kayan Kula da Gandun Daji ta Tarayya (FCFM), Afaka, da ke unguwar Mando sun ce ana fargabar ’yan bindigar sun yi awon gaba da kusan rabin dalibai mata da ke makarantar.
- NAFDAC ta yi gargadi kan bullar rigakafin COVID-19 na bogi
- Nan ba da jimawa ba jirgin kasan Kano Zuwa Legas zai dawo aiki —NRC
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda reshen Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya shaida wa Aminiya cewa: “An yi garkuwa da su ne a cikin dare, amma babu bayani game da yawansu, kuma ba zan iya cewa ba ko dukkansu mata ne”.
Ya kuma ce suna aiki tare da sojoji wajen bin sawun masu garkuwar da kuma kubutar da daliba.
Shi ma da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ce sun riga sun isa kwalejin don tantance hakikanin abun da ya faru.
Mazauna sun tabbatar da jin karar hare-hare a cikin dare, amma sun dauka daga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta NDA ne.
Mando unguwa ce mai makwabtaka da NDA da Babban Filin Jirgin Sama na Kaduna a bangare guda, da kuma Barikin Sojin Sama daga daya bangaren.
Aminiya ta kuma gano cewa tuni jami’an tsaro sun isa makarantar sun kuma fara bincike yayin da jirgi ke shawagi don gano inda aka bi da wadanda aka sacen.
Harin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan umarnin Shugaba Buhari ga jami’an tsaro cewa su bindige duk wanda aka gani dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba.
A lokacin ne kuma ba wa Manyan Hafsoshin Tsaro wa’adin mako shida, wato kafin faduwar damina, su shawo kan matsalar ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Gabanin harin Buhari ya yi alkawarin cewa sace dalibai mata 279 da ‘yan bindiga suka yi a makarantar sakandaren GGSS Jangebe, Jihar Zamfara, shi ne zai zama karon karshe da aka yi garkuwa da dalibai a Najeriya.