Masu garkuwa da mutane sun sako wata mata mai danyen maijego, mako biyu bayan sun dauke ta daga gidan mijinta.
’Yan bindigar sun sace Zainab Buba ce bayan ta haihu da kwana hudu a kauyen Namne da ke Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.
- Jadawalin Gasar Firimiyar Ingila na Makon farko
- Karin kudin mai da wuta: Buhari ya bukaci tattaunawa da ’yan kwadago
Majiyar Aminiya ta ce ’yan bindgar sun sako matar ce bayan mijinta, Buba Maianguwa ya biya su kudin fansa Naira dubu dari uku.
Aminiya ta kuma gano cewa ’yan bindigar da suka yi garkuwa da Sakataren Kungiyar Manoman Shinkafa (RIFAN) reshen Jihar ta Taraba, Malam Mamman Rabiu sun sako shi.
Shi ma mako biyu da suka wuce aka yi garkuwa da shi kuma ba a sako shi ba sai da iyalansa suka biya kudin fansa.
Sai dai kuma har yanzu ba a sako wani malami Kwalejin Fasaha ta Jihar Taraba da aka yi garkuw da shi ba.
Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba ne da Kamaludeen Aliyu Babando ne kwana biyar da suka gabata a gidansa da ke kusa da Asibitinn Kwararrun na Jalingo.
Rahotanni na cewa iyalansa na tattaunawa da ’yan bindigar da neman kudin fansa Naira miliyan 20.
Matsalar garkuwa da mutane na karuwa a Jihar Taraba musamman a garin Jalingo da wasu yankunan karkara.
Kananan hukumomin da abun ya fi kamari sun hada da Jalingo, Gassol, Bali, Ardo, Kola, Lauda Karim Lamido.
Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Taraba, DSP David Misal ya tabbatar a Aminiya cewa ’yan sanda na yin iya kokarinsu domin takaita matsalar ta garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a fadin jihar.