A yau Alhamis ‘yan bindiga sun sako Hakimin gundumar ’Yan Kaba Alhaji Buhari Ammani, tare da iyalansa sakamakon taron tattaunawar zaman lafiya da aka yi tsakanin masu aikata yin garkuwa da mutane da gwamnatin jihar Zamfara.
An yi garkuwa da Basaraken ne tare da iyalansa kimanin wata uku da suka wuce a unguwar ‘Yan Kaba da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda a jihar.
Mai taimakawa Gwamnan jihar Zamfara Bello Mutawalle, na musamman a harkokin tsaro Abubakar Mohammed Dauran, wanda ya karbi Hakimin daga hannun masu garkuwan bayan an sako shi, ya ce kimanin wata uku kenan da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da Hakimin tare da iyalansa. Ya kara da cewa, wannan babban nasara ce da wannan gwamnatin jihar ke samu a yanzu.