Kasa da awa 24 bayan ’yan bindiga sun sace wani jaririn da wata mai jego ta haifa a sansaninsu, an sake kashe mutum uku tare da sace wasu 16 a kauyuka uku na Karamar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna.
Wani mazaunin yankin, Shehu Rabi’u, wanda ya tabbatar wa Aminiya faruwar harin ta wayar salula ranar Laraba, ya kuma ce an kai hare-haren ne a kauyukan Kala da Kutar da kuma Taka-Lafiya.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ake shirin kammala zaben Gwamna a Adamawa
- An ragargaza baburan ’yan acaba 476 da aka kwace a Abuja
Ya ce maharan, wadanda ke kan babura dauke da bindigu kirar AK-47, da farko sun kai hari ne kan wani matsugunin makiyaya da ke Taka-Lafiya, inda suka sace mutum shida, sannan suka kashe wani mai suna Malam Ya’u.
Ya ce daga nan ne maharan suka wuce kauyen Kutar mai makwabtaka da shi, inda a can ma suka yi awon gaba da mutum bakwai.
Kazalika, Shehu ya ce ’yan bindigar sun kuma karasa kauyen Kala suka sace mutum biyar bayan sun yi ta harbe-harbe.
“A lokacin da suke ta harbe-harben ne mutum biyu suka mutu a Taka-Lafiya, daya kuma a Kutar,” in ji Shehu.
Shi ma Madakin Janjala, wani kauye da ke da makwabtaka da inda aka kai hare-haren, Sama’ila Babangida, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa Jere lokacin da ya samu labarin.
Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar dai na da sansanoninsu a Tagwayen Dutse, wani dajin gwamnati da ke tsakanin Kananan Hukumomin Kagarko da Kachia na jihar Kaduna.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wani karin bayani kan batun daga Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kadunan.