✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake kashe mutum 10 a kauyen Birnin Gwari

“Mun kira jami'an tsaro amma ba su zo ba sai da gari ya waye bayan maharan sun gama cin karensu ba babbaka.”

Kasa da sa’o’i 48 bayan ’yan bindiga sun hallaka mutum 18 a kauyen Kutemeshi, mahara sun sake kashe mutum 10 a kauyen Anguwar Gajere na yankin Kutemeshin a Karamar Hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewa an fara kai harin ne da misalin karfe 6:00 na yammacin Litinin, inda ’yan bindigar suka ci gaba da ruwan wuta na kusan sa’a uku ba kakkautawa.

Maharan dai sun yi wa garin tsinke ne a kan babura sannan suka rika harbin kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su yashe ilahirin shagunan garin.

Da yake tabbatar da lamarin, Kansilan mazabar Kutemeshi, Adamu Salisu ya ce ’yan Kato-da-gora na yankin sun yi iya bakin kokarinsu wajen tunkarar maharan.

“A sakamakon haka, 10 daga cikin mutanenmu sun mutu a harin da aka kawo tsakanin karfe 6:00 na yamma zuwa 9:00 na dare.

“Karin wasu mutum hudu kuma sun ji munanan raunuka saboda harbin su da aka yi.

“Mun kira jami’an tsaro daga garin Dogon Dawa, amma ba su zo ba sai da gari ya waye bayan maharan sun gama cin karensu ba babbaka,” inji Kansilan.

Ya ce zuwa yanzu ba a kai ga binne mutanen da suka rasu ba.

Wani mazaunin yankin, Malam Sagiru ya ce sun shiga matukar dimuwa lokacin da ’yan bindigar suka yi wa garin kawanya, ko da yake ya ce su ma sun samu nasarar kashe daya daga cikinsu.

Ya kuma ce wani jirgin yaki ya yi shawagi a yankin, mintuna kadan bayan ’yan bindigar sun gudu.

Da muka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce suna sane da harin kuma Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar na kan hanyarsa ta zuwa yankin.