✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sake kai hari Neja, mutum 18 sun fada tarko

Yanzu kauyuka sun zama fayau a yankin.

’Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kapana na Karamar Hukumar Munya da ke Jihar Neja, inda suka kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da mutum 18 baya ga wadansu da dama da suka raunata.

Mazauna yankin kamar yadda wata majiya daga cikinsu ta ruwaito, ta bayyana cewa maharan sun afka musu ne a daren Talata inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi domin su firgita.

Ta ce mazauna yankin da lamarin ya zo musu a bazata, sun shiga neman mafaka inda a nan karar kwana ta cimma wani daga cikinsu yayin da kuma da dama suka tsallake rijiya da baya da raunuka na harsashin bindiga.

Kazalika, ta ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da wadanda suka yi rashin sa’ar tserewa musamman mata da kananan yara.

Aminiya ta samu cewa, kauyen da lamarin ya shafa da kuma na kewayen da ke makwabtaka sun zama fayau babu mutane a yayin da al’ummominsu suka sauya sheka zuwa wasu wuraren mafi aminci.

Dan Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar mazabar Munya Mista Andrew Danjuma Jagaba wanda ya bayar da tabbaci kan aukuwar lamari, ya yi Allah wadai da harin da ’yan bindigar suka kai cibiyarsa.

Ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su tsananta tsaro a yakin domin dakile aukuwar makamancin wannan lamari a gaba.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsa a kan cewa gwamnati za ta yi duk wata mai yiwuwa wajen daukan matakin da ya dace.

Haka kuma, ya jajanta wa ’yan uwan wadanda suka mutu da wadanda suka ji rauni da kuma wadanda aka yi garkuwa da su, yana mai cewa gwamnati za ta yi ruwa da tsaki a lamarinsu.

Sai dai neman jin ta bakin jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya ci tura a yayin tattaro wannan rahoto.