’Yan bindiga sun sake kai farmaki kauyen Albasun Liman Sharehu, da ke Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da mutum tara.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da sanyin safiyar ranar Laraba.
- An sace amarya da ango bayan mako daya da bikinsu a Katsina
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 48, sun kashe 2 a Katsina
- Za mu kawar da ayyukan ta’addanci a Katsina —Shugaban ’Yan Sanda
- ’Yan bindiga sun sace mutum 16 a kauyen Katsina
Wakilinmu ya ruwaito cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, har da dalibin aji biyu na Babbar Sakandire ta Damari da kuma mahaifinsa.
Idan ba a manta ba, ko a ranar Kirsimeti sai da ’yan bindigar suka kai farmaki kauyen, inda suka yi garkuwa da mutum takwas ciki har da matan aure biyu.
Sai dai mutum takwas din da aka yi garkuwa da su a satin da ya gabata sun tsere yayin da ’yan bindigar ke barci.
A cewar wata majiya daga kauyen, ’yan bindigar sun fusata ne suka sake dawowa sakamakon tserewar mutanen.