✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 21 ’yan gida ɗaya a Zamfara

’Yan bindigar sun yi awon gaba da fiye da mutum 40 a ƙauyen Kasuwar Daji da ke Karamar Hukumar Ƙauran Namoda a Zamfara.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da fiye da mutum 40 a ƙauyen Kasuwar Daji da ke Karamar Hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su har da wasu mutum 21 ’yan gida ɗaya da masu garkuwar suka yi wa shigar ba zata.

Wani dan uwan waɗanda abin ya shafa ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai harin na ramuwar gayya ne da sanyin safiyar yau Talata.

A cewarsa, mutum 21 da ke da dangantaka ta jini sun haɗa da iyalan wani tsohon Shugaban Ƙungiyar Motocin Haya, Alhaji Hamisu Kasuwar Daji, wanda ’yan bindigar suka yi awon gaba da matansa biyu da ’ya’ya 13 da wani ƙaninsa da sauran ’yan uwa.

Ya kara da cewa, an kashe ’yan sanda biyu yayin harin da ’yan bindigar suka shafe tsawon sa’a uku suna cin karensu babu babbaka.

“Suna isowa ƙauyen suka fara da ofishin ’yan sandan da ke kusa da gidan Alhaji Hamisu Kasuwar Daji.

“Daga nan suka garzaya gidan suka yi awon gaba da matansa biyu. Sai dai matarsa ta uku ta tsallake rijiya da baya wadda ba su samu sa’ar shiga ɗakinta ba

“Sai dai sun lalube duk wani lungu da saƙo na gidan, inda suka tattara duk ahalinsa suka ƙara gaba.

Hakan na zuwa ne kimanin mako biyu bayan da gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya ƙaddamar da rundunar Askarawan Zamfara, waɗanda za su taimaka wajen yaƙi da matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.

Zamfara na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro, inda ƴan bindiga ke far wa ƙauyuka suna kashewa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.