✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutum 12 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace mutum 12 a wani sabon hari da suka kai Karamar Hukumar Kachia.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutum 12 yayin wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai mahadar Awon/Mothercat da ke Karamar Hukumar Kachia ta jihar.

Jami’in Hulda da Al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an ceto mutum biyu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

A cewarsa, “Da misalin karfe 9 da minti 20 na daren ranar Laraba muka samu rahoton wasu ’yan bindiga da ba a kai ga gano ko su waye ba dauke da mugggan makamai sun mamaye mahadar Awon/Mothercat inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi a yayin da jama’a ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

“Bayan samun rahoton ne muka tura wata tawagar hadin gwiwa da ’yan sanda da sojoji da ’yan banga wadanda suka tunkari wajen da nufin dakile harin, sai dai da isarsu suka tarar sun yi wa wasu mutum hudu rauni yayin da kuma sun kashe wani mutum mai kimanin shekaru 40 a duniya.

“Sai dai abin takaicin shi ne ’yan bindigar sun yi awon gaba da mutum 14 yayin da kuma aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti,” inji ASP Jalige.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Kakakin ’yan sandan yana cewa, jami’an tsaron sun fatattaki ’yan bindigar har zuwa wajen gari sannan suka ceto mutu biyu yayin da suka yi awon gaba da ragowar mutum 12.

A yayin da ya tabbatar da cewa tarzoma ta lafa kuma an ci gaba da al’ummar kamar yadda aka saba  yankin, ASP Jalige ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ceto ragowar wanda ke hannun ’yan bindigar cikin koshin lafiya.