✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutane 150 da shanu 1,000 bayan kisan Sarkin a Gobir

Sun sace mutane 150 da shanu kimanin 1,000 kwanaki ƙalilan bayan sun hallaka Sarki Isa Muhammad Bawa

Aƙalla mutane 150 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Masarautar Gobir da ke Jihar Sakkwato.

’Yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da shanu sama da 1,000 a yayin harin da suka kai ƙauyukan yankin.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa, Hon. Amini Boza, ya bayyana cewa an sace aƙalla mutane 151 a tsakanin yankin Sabon Birni da Yanfaruna.

Aminu Boza ya ce, washegarin kisan Sarkin Gobir ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye suka kashe mutane suna sace wasu da ba a tantance adadinsu ba.

Ya ce a kauyen Yanfaruna an sace mutane 22 da ƙarin mutane 11 a ƙauyen da ke gaba da shi.

“Saboda haka, akalla mutane 192 aka sace kuma har yanzu suna hannun ’yan bindiga,” a cewarsu.

Shi ma da yake tabbatar da sace mutanen, Farfesa Bello Bada na Jam’iyar Usmanu Ɗanfodiyo, ya bayyana takaici bisa yadda ’yan ta’addan suka sake kai harin mummunan harin bayan sun kashe Hakimin yankin.

Ya ce, babban abin takaicin shi ne wasu fitattun mutanen yankin suna iya kiran waya ’yan ta’addan su tattauna da su.

“Dalili kuwa shi ne an san ’yan ta’addan, kuma mutanen yankin sukan tattauna da su; saboda haka mutanen yankin sun san ko su wane ne.

“In ba haka ba, ya aka yi ’yan bibdiga suke iya shiga kasuwanni sun sayar da shanun sata a yankin.

“Ya aka yi ’yan bindiga suka sace shanu 1,000 a yankin? Shin fukafuki ne da shanun ko me.

“Ina bayanan sirri da ake tattarawa? Ta yaya ’yan bindigar ke ratsawa yankin ba tare da an gan su ba?”

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ’yan ta’addan sun hallaka Sarki Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa. wanda shi ne Hakimin Gatawa ne bayan ya shafe kwanaki a hannunsu.

Sun sace basaraken ne tare da dansa da wasu mutane shida a hanyar Sakkwato zuwa Sabon Birni.