✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace malamin jami’a a Taraba

Wadansu ’yan bindiga sun sace tare da yi garkuwa da wani babban malami a Jami’ar Jihar Taraba, Mista Benjamin Ezekiel. Bayanai sun ce zuwa hada…

Wadansu ’yan bindiga sun sace tare da yi garkuwa da wani babban malami a Jami’ar Jihar Taraba, Mista Benjamin Ezekiel.

Bayanai sun ce zuwa hada wannan rahoto, wadanda suka sace malamin ba su tuntubi iyalansa ba, kwanaki bayan  yin garkuwa da shi, lamarin da ya haifar da  fargaba game da lafiyarsa.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar da ba a tantance ko su wane ne ba sun yi awon gaba da Mista Ezekiel a rukunin gidajen jami’ar da ke ATC, kusa da makarantar Grace Junior Academy da jijjifin safiyar Lahadin da ta gabata.

Garkuwa da malamin na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamnan Jihar, Ishaku Darius ya rattaba hannu a kan dokar hukuncin kisa a kan wanda aka kama da laifin garkuwa da jama’a; yayin da za a yi daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin yunkurin yin garkuwa da mutane.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Dabid Misal ya ce rundunar na  bakin kokarinta wajen ganin an ceto malamin.

Aminiya ta fahimci cewa wannan ne karo na biyu da ake yin garkuwa da ma’aikacin jami’ar Jihar Taraba. Ma’aikaci na farko da aka sace a baya, shi ne Mataimakin Magatakardar Jami’ar, Malam Sanusi Sa’ad kuma sai da aka biya wasu kudaden da ba a bayyana adadinsu ba; kafin sako shi.