Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutum takwas tare da sace Dagacin kauyen Guga, Dan Alhaji Umar, da ke Karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, da ’yan bindiga suka yi.
Da ya ke tabbatar da faruwar harin, kakakin ’yan sandan Jihar, SP Gambo Isah, ya ce ’yan bindigar sun kai farmakin kauyen da misalin karfe 10:00 na dare inda suka dinga harbi a iska, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum hudu sannan suka sace wasu hudu.
- A shirye muke mu mika Abba Kyari ga Amurka idan bukatar haka ta taso — Malami
- Mutum miliyan 13 na fuskantar barazanar yunwa a Afirka – MDD
Ya kara da cewar a kan hanyarsu ta komawa, ’yan bindigar sun yi dauki ba dadi da ’yan sa-kai a Unguwar Galadima, wanda a nan ma suka kashe hudu daga cikin ’yan sa-kan, sannan suka raunata wasu.
Kazalika, rahotanni daga yankin na nuna cewar wanda suka samu rauni sun haura mutum 10.
Daya daga cikin ’ya’yan mai garin dai ya rasa ransa a sakamakon harin, kuma iyalansa sun ce maharan ba su tuntube su ba, bare su ji ta bakinsu.
Wata majiya daga kauyen ta ce wannan shi ne karo na farko da mahara suka taba kai hari kauyen na Guga.
Majiyar ta kuma ce, ’yan bindigar sun kone shaguna da dama a kauyen sannan mutane da yawa sun bace, kuma ba a da tabbacin sace su aka yi ko kuma bacewa suka yi.
Har wa yau, majiyar ta ce an sace daya daga cikin iyalan dan takarar shugabancin Karamar Hukumar a jam’iyyar PDP.
A wani labarin kuma, kakakin ’yan sandan Jihar, ya ce wasu mahara sun farmaki kauyen Yar’aikau da ke Karamar Hukumar Musawa, inda suka sace mutum daya sannan suka yi awon gaba da dabobbi.
Sai dai ya ce jami’an ’yan sanda sun yi nasarar ceto mutumin da dabbobin da maharan suka sace a kauyen.