✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace likita yana tsaka da aiki a asibitinsa a Adamawa

Wata majiya ta ce dududu harin bai wuce minti biyar ba.

Yan bindiga sun kutsa kai wani asibiti da ke Yola, babban birnin Jihar Adamawa da yammacin ranar Litinin, inda suka sace mamallakinsa.

Mutumin, mai suna Dokta Sa’idu Bala dai tsohon Shugaban Asibitin Kwararru na Yola ne.

A cewar wata majiya, ’yan bindigar sun mamaye asibitin ne wajen misalin karfe 6:00 na yamma, lokacin da ake Sallar Magriba.

Majiyar ta ce suna shiga asibitin ba su yi wata wata ba, suka fara harbin iska don su razana mutane.

“Daga nan sai suka wuce kai tsaye zuwa ofishinsa sannan suka gudu da shi. Dududu harin bai wuce minti biyar ba,” inji majiyar.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da kai harin, inda ya ce tuni suka aike da dakarunsa don ceto likitan da kuma kama masu garkuwar.

“Jami’annu sun samu albarusai uku da aka yi amfani da su a wurin, kuma mun baza su don kama masu garkuwar da ceto mutumin.