✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace Kwamishina a Neja

An yi garkuwa da shi da misalin karfe 1 na daren ranar Litinin.

Wasu ’yan bindiga sun sace Kwamishinan Yada Labara na Jihar Neja, Alhaji Muhammed Sani Idris.

Rahotanni sun bayyana an sace Idris gidansa da ke garin Baban Tunga da ke Karamar Hukumar Tafa ta jihar da sanyin safiyar Litinin.

  1. Kwalara ta kashe mutum 60 a Katsina
  2. Majalisa ta gindaya sharudan kirkirar sabbin jihohi

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da cewa an sace Kwamishinan da misalin karfe 1 na daren Litinin.

A cewarsa, tuni jami’an tsaro suka bazama a kokarin kubutar da shi ba tare da wani abu ya same shi ba.

Ya ce, “An yi garkuwa da shi da sanyin safiyar yau da misalin karfe 1 na dare a Baban Tunga a Karamar Hukumar Tafa.

Aminiya ta rawaito cewa har kawo yanzu wadanda suka yi garkuwa da Kwamishinan ba su tuntubi iyalansa ba ko wani makusancinsa game da batun biyan kudin fansa.