✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace Hakimi da tsohon Sakataren ilimi a Kaduna

Wasu da ake zaton ‘yan ta’addan Birnin Gwari ne sun sace Hakimin tsakiyar garin Birnin Gwari Alhaji Abubakar Yahaya. Har ila yau ‘yan ta’addan sun…

Wasu da ake zaton ‘yan ta’addan Birnin Gwari ne sun sace Hakimin tsakiyar garin Birnin Gwari Alhaji Abubakar Yahaya.

Har ila yau ‘yan ta’addan sun kuma sace tsohon sakataren ilmi na karamar Hukumar Ibrahim Musa, wanda yake tare da Hakimin.

Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya auku ne a kusa da Labi a akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Kuma lamarin ya auku ne da misalin karfe 12 na ranar a yau Laraba.

Wata mijiya ta mu wanda bata san a ambaci suna ya shaida mana cewa, lamarin ya jefa al’ummar garin Birnin Gwari cikin damuwa.

“Suna tare a cikin mota ne lokacin da ‘yan ta’addan suka far Masu har suka dauke su watau Hakimin tsakiyar Gari da kuma shi tsohon sakataren ilmi wanda aka fi Sani da Ibrahim ES,” in ji shi.

Kakakin ‘yan sandan jihar Yakubu Sabo, ya ce zai yi bincike akan lamarin kafin ya ce wani abu.