’Yan bindiga sun yi awon gaba da wani DPO din ‘yan sanda da aka tura aiki kwanan nan zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin.
- ‘Abin da ya sa muka kashe Ahmed Gulak’
- Hajji 2022: Rukunin farko na maniyyatan Kano za su tafi Saudiyya ranar Litinin
Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kama sabon aikinsa a lokacin da lamarin ya faru.
Sai dai kawo yanzu babu tabbaci ko jami’in na tafiya ne shi kadai a cikin motar lokacin da aka dauke shi ba.
Har yanzu dai ’yan sanda ba su ce uffan ba ballantana fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Da aka tuntubi Mohammed Jalinge, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ya ce, “Zan binciko lamarin tukunna.”