✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Bindiga Sun Sace Dagattai 2 A Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa an sace dagattai biyu da ke kan hanyarsu daga Kakangi zuwa Birnin-Gwari. ’Yan bindiga sun kuma kai hari a…

Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa an sace dagattai biyu da ke kan hanyarsu daga Kakangi zuwa Birnin-Gwari.

’Yan bindiga sun kuma kai hari a Maraban Agyaro inda suka sace wasu mutane a Kakangi da Kisaya, suka kashe wasu mutane takwas a karamar hukumar ta Birnin Gwari.

Maharan sun kai harin yankin ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Alhamis, inda suka  yi awon gaba da wasu manoma hudu da ke aiki a gonakinsu.

Wata majiya a yankin ta ce an sace mata shida a kauyen.

Dan majalisar da ke wakiltar gundumar Kakangi a majalisar dokokin jihar, Yahaya Musa Dan Salio, ya ce dukkan mutane takwas da aka kashe ’yan Kakangi ne.

“Eh, yanzu ne aka yi min waya cewa an sace mutum biyu a mazabata tare da kashe wasu takwas. Duk wadanda aka kashe ’yan Kakangi ne,” in ji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ce zai yi bayani idan ya kammala bin diddigin abin da ya faru a yankin.