Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken garin Gindiri da ke Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Aminiya ta gano cewa maharan dai sun sace basaraken be a cikin gidansa bayan sun yi harbe-harbe da sanyin safiyar ranar Lahadi.
- Jagora a yaki da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, Desmond Tutu, ya rasu
- ‘Rashin adalcin shugabanni ne tushen matsalar rashin tsaro a Najeriya’
Manjo Ishaku Takwa, Kakakin rundunar tsaro ta ‘Operation Safe Haven’ (OPSH), wacce ke aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin, shi ne ya tabbatar da hakan.
Sai dai ya ce tuni rundunar ta baza dakarunta a yankin kuma suna nan suna bin diddigin masu garkuwar.
Ya sha alwashin cewa za su kubutar da shi nan ba da jimawa ba daga hannun wadanda suka sace shin.