✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun rage kudin fansar kananan yaran da suka sace a Kaduna

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da kananan yara hudu ’yan gida daya a Kaduna sun rage kudin fansar da suke nema daga Naira miliyan…

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da kananan yara hudu ’yan gida daya a Kaduna sun rage kudin fansar da suke nema daga Naira miliyan 300 zuwa miliyan 25.

A ranar Talata da ta gabata ne ‘yan bindiga suka kutsa cikin gidan a unguwar Keke A a yankin New Millennium City da ke Karamar Hukumar Chikun suka yi awon gaba da yaran.

Sun sace yaran ne a yayin da mahaifin ya je dubiyar mahaifiyarsu da ke jinyar kannensu tagwaye a asibiti da misalin karfe 9 na dare.

Tun wannan lokacin yaran suke hannun ‘yan bindigar, wadanda daga bisani suka tuntube mahaifin suna neman kudin fansa Naira miliyan 300, tare da barazanar halaka yaran, masu shekaru biyu, tara 12 da kuma 14.

Masu garkuwar sun yi baranzara kashe na mijin da ke cikin yaran wanda shi ne dan karami, saboda a cewarsu ya dame su da kuka.

A ranar Litinin mahafinsun ya shaida wa wakilinmu ceaw an rage kudin fansan da ake nema zuwa Naira miliyan 25, kuma ba shi da su.

Tun bayan da aka sace yaran iyayensu ke rokon mahukunta su taimaka su ceto su cikin koshin lafiya, suna masu kira ga al’umma da su taya su da addu’o’i da duk abin da za su iya domin Allah Ya kubutar da ’ya’yan nasu.