✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda a Jigawa

Kasa da mako guda bayan ’yan bindiga sun kashe wani dan sanda a Jihar

Akalla ’yan sanda biyu ne suka rasa bakunci lahira a wani artabu da suka yi da ’yan bindiga a Karamar Hukumar Garki, Jihar Jigawa.

Dauki-ba-dadin na ranar Juma’a ya kuma yi sanadin jikkata da sanda daya yayin artabunsu da ’yan bindigar a rugar Fulanin Kalgo.

Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, Audu Jinjiri, ya ce bayan samun rahoton ayyukan ’yan bindiga ne suka farmake su, amma ’yan bindigar sun bindige jami’ansu biyu.

Jinjiri ya kara da cewa sun samu gawar daya daga cikin ’yan bindigar da aka harba, bayan da ’yan sanda suka fatattake su.

’Yan bindiga sun yi garkuwa, sun kashe jami’in tsaro

Kasa da mako guda ke nan da wasu ’yan bindiga suka kashe jami’in tsaro a Karamar Hukumar Maigatari ta Jihar Jigawa.

A cewarsa, dan sandan da aka kashe ya yi kokarin ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su ne a yankin Bosuwa.

Rundunar ta kara da cewa, ’yan bindigar sun yi garkuwa da Ali Dankoli mai shekara 70 da kuma Zainab Isah mai shekaru 25, mazauna Bosuwa.

Sai dai a ranar Juma’ar da ta gabata sun saki Zainab bayan an biya kudin fansa da a bayyana ba.