Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen ‘Yarbulutu da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka kashe wasu ‘yan sanda uku tare da wasu mutum uku.
An ruwaito cewar sun kai harin ne da misalin karfe 2:30 na rana, yayin da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar ta Sakkwato don halartar wani taro.
- Buhari Ne Ya Gina Hanyar Garinku, Ya Kori Boko Haram —APC Ga Atiku
- Bidiyon Dala: Ganduje da Jaafar Jaafar sun hadu a London
Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun bude wuta kan wasu ‘yan kasuwa da ba su ji ba ba su gani ba, a wata kasuwa da ke ci mako-mako, lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa.
Ya ce maharan sun kashe jami’an ‘yan sandan uku ne bayan da suka kai dauki kasuwar lokacin da suka ji harbe-harbe na tashi.
Kazalika, ya ce sun kone wasu motoci biyu da ‘yan sandan ke amfani da su a wani shingen bincikensu.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta samu rahoton kuma suna kan farautar maharan domin kamo su.
Wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren’yan bindiga ke dada kamari a yankin.
Ya ce Kananan Hukumomin Sabon Birni da Isa da ke gabashin Jihar na ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga.
Idan ba a manta ba, ko a makon jiya sai da wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe mutum shida a wani kauye na Karamar Hukumar Goronyo ta jihar.
Jihar Sakkwato na daga cikin Jihohin Arewa da ke fuskantar barazanar hare-hare daga ‘yan bindiga, wanda hakan ya tilasta wa dubban jama’a yin kaura daga yankunansu.