’Yan bindiga sun hallaka akalla sojoji 22 da ’yan sanda 7 a wasu hare-hare da suka kai Jihohin Neja da Taraba.
Akalla sojoji 15 ne suka kwanta dama a wani harin kwanton bauna da suka kai musu a kan hanyarsu ta kai dauki kan wani harin da aka kai wajen hakar ma’adinai na wasu ’yan kasar China a Jihar Neja.
- Za mu gurfana a kotu da wanda ya yi min kazafi —Kamaye
- Kungiyar Kwadago ta kira zanga-zanga kan yajin aikin ASUU
Bayanai sun ce sojojin da aka kashe na Bataliya ta 45 ne da ke Bida, kuma suna kan hanyarsu ta kai daukin gaggawa ne ga wani kamfanin hakar ma’adinai na wasu ‘yan Chaina a Karamar Hukumar Shiroro da ke Neja.
Haka kuma, a yayin harin ne aka kashe ‘yan sanda bakwai da wasu sojoji da ke gadin wurin, inda kuma yi awon gaba da ‘yan Chinan da ke wurin a ranar Laraba.
A wani labarin mai nasaba da wannan da Aminiya ta samu, wasu ’yan bindiga sun kashe sojoji bakwai a wani hari da suka kai Jihar Taraba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa harin na kwanton bauna ya yi ajalin sojojin ne a dajin Amdami da ke Karamar Hukumar Karim Lamido ta Jihar Taraba.
‘Mun shiga farautar masu hannu a wannan aika-aika’
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce soma farautar ’yan ta’addan da suka kashe jami’an tsaro da fararen hula a yayin harin da suka kai wurin hakar ma’adinai a Jihar Neja a ranar Laraba.
Babban Hafsan Sojin Kasan, Laftanar-Janar Faruk Yahaya ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Juma’a.
Da yake jawabi a masallacin Barikin Mogadishu jim kadan bayan kammala sallar Juma’a, inda aka gudanar da addu’o’i na musamman na bikin cika shekaru 159 da kafa rundunar sojin, Laftanar-Janar Yahaya ya ce dakarun sojin Najeriya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin masu hannu a wannan aika-aika sun girbi abin da suka shuka.
Babban Hafsan Sojin wanda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika yaba wa kwazon sojoji da kullum suke fadin tashin ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa dunkulalliya, ya kuma bukaci jama’a da su tabbatar sun yi addu’a ga sojojin da suka rasa rayukansu a kokarin kare martabar kasar nan.