’Yan bindiga sun kashe mutum takwas a harin da suka kai kauyen Janbako da ke Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara ranar Lahadi.
Mazauna sun ce ’yan bindiga sun dirar wa garin ne da misalin 10:30 na safe a kan babura suka rika harbin jama’a barkatai.
- ’Yan kasuwar Kano da aka yi garkuwa da su sun kubuta
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- An kama kwarto ya haka ramin da ke kai shi gidan auren tsohuwar budurwarsa
- An kama ’yan uwa 3 sun kashe mai gadi
“An shiga rudani a kauyen inda mutane suka yi ta guje-gujen neman tsira da rayuwarsu duk da cewa ’yan banga sun yi kokari sun kashe wasu daga cikin maharan.
“Dole ta sa muke samar ’yan banga masu dauke da makamai domin su kare mu da kuma wadanda suka je makabarta domin binne mamatan.
“Akasarain mamatain an kashe su ne a yayin da suke kokarin tserewa daga harin saboda maharan na harbi ne kan mai uwa da wabi.
“Mun gode Allah jami’an tsaro sun yi saurin kawo dauki, amma da abin sai ya fi haka muni,” inji wani mazaunin kauyen.
Wakilinmu bai kai samu jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara ba, SP Muhammad Shehu, zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.