✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun sace Dagaci a Kano

Rahotanni sun ce maharan sun zo ne a kan wasu babura guda uku

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum shida a garin Karfi na Karamar Hukumar Takai da ke Jihar Kano.

Takai dai na da nisan kimanin kilomita 80 a Kudancin Kano, kuma ta yi iyaka da garuruwan Jihar Jigawa.

Rahotanni sun ce maharan sun kai farmaki ne garin Karfi da ke Karamar Hukumar da yammacin Lahadi, sannan suka sace Dagacin garin mai kimanin shekara 53, Abdul Yahaya Ilo.

Maharan dai an ce sun zo ne a kan wasu babura guda uku daga Jihar Bauchi, ta garin Ringim da ke Jihar Jigawa.

Bayanai na nuni da cewa suna kan hanyar ficewa daga garin ne bayan dauke Dagacin ’yan sa-kai suka bi sahunsu da nufin kubutar da mutanen.

Sai dai ’yan bindigar sun juyo da baya inda suka bude wuta suka harbi mutum tara, inda aka tabbatar da mutuwar mutum shida daga cikinsu.

Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni suka aike da dakarunsu zuwa yankin don ceto Dagacin da kuma kama maharan.