✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Kaduna

’Yan bindigar sun kawo mana farmaki da misalin karfe 11:00 na safiyar Juma'a inda suka kashe mutum hudu.

‘Yan bindiga sun kashe mutum shida ciki har da karamin yaro dan shekara bakwai a Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna. 

Aminiya ta ruwaito cewar mutane kauyen 20 ne suka samu raunukan harbin bindiga a farmakin da aka kai da misalin karfe na safiyar ranar Juma’a.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren Kungiyar Ci Gaban Matasa ta Kidandan, Jamilu Hussaini Kidandan, ya ce kawo yanzu an nemi mutanen kauyen da dama an rasa.

Ya ce, yawanci mutanen kauyen sun gudu sun bar gidajensu tun bayan aukuwar harin.

“’Yan bindigar sun kawo mana farmaki da misalin karfe 11:00 na safiyar Juma’a inda suka kashe mutum hudu.

“Sun kuma dawo yau Asabar inda suka kashe mutum biyu, daga ciki har da yaro dan shekara 7,” inji shi.

Shugaban matasan ya ce an kai mutum 20 da aka harba da bindiga Asibitin Kwararru na Shika da Asibitin Shafi’iya da ke garin Zariya.

Kakakin Rudunar ’Yan sanda na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an tura motocin yakin ’yan sanda 3 zuwa garin.