✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 22 a Birnin Gwari

’Yan bindiga sun harbe mutum uku taer da sace wasu 22 a kauyukan Karamar Hukumar Birnin Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun harbe mutum uku taer da sace wasu 22 a kauyukan Karamar Hukumar Birnin Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

A ranar Asabar da almuru maharan suka far wa kauyen Hayin Gada da ke Damari, suka bindige wasu mutum biyu, suka sace wasu 12 tare da fasa shaguna su kwashe kayayyaki.

Shugaban Kungiyar Cigaban Al’ummar Birnin Gwari (BEPU) Ishaq Usman Kasai, ya shaida wa wa Aminiya a safiyar Litinin cewa a ranar Asabar din, ’yan bindigar sun kashe mutum daya tare da sace wasu shida a yankin Farm Centre da ke hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Sun kuma yi sace mutum hudu a Dajin Jangali tare da sace wa wasu manoma babura uku a yankin Kamfanin Doka.

“’Yan bindiga na kara cin karensu babu babbaka inda suke fasa shaguna suna sace kaya Birnin-Gwari.

“Ba za mu daina kira ga hukumomin da suka kamata domin su kara azama wajen yakar ’yan ta’adda da suka hana yankin Birnin Gwari sakat, musamman yanzu da aka kusa girbe amfanin gona,” in ji shi.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sadan Jihar kaduna, DSP Jalige Mohammed, kan batun, amma ya yi alkawarin zai tuntubi yankin sannan waiwaye shi daga baya.