✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a Legas

Maharan sun kashe mutanen uku sannan suka tsere.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun kashe mutum uku a rukunin gidajen Gowon da ke unguwar Ipaja a jihar.

Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Alhamis cewa ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 11:35 na dare.

Ya ce, ofishin ’yan sanda na yankin ya samu kiran gaggauwa cewar wasu ’yan bindiga sun harbe wasu mutane a cikin wani gida.

Wani ganau ya ce nan da nan maharan suka bar rukunin gidajen bayan harbe mutanen.

Hundeyin ya ce an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Igando.

“Bayanan da ’yan sanda suka samu sun nuna cewa ’yan uwan biyu daga cikin wadanda suka mutu sun dauke su.

“Wani mutum da ya tsira daga harin, Doba Ngoze, yanzu haka yana kwance a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas, da ke Idi-Araba,” in ji shi.

Kakakin ya ce tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin.