✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace 50 a kauyen Kaduna

Maharan sun shafe awa biyu suna cin karensu babu babbaka, inda suka shiga gidaje 13

’Yan bindig suna hallaka manoma biyu suka kuma sace wasu mutum 50 a kauyen Unguwar Gimbiya da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Shaidu sun ce maharan dauke da muggan makamai sun kai farmakin ne a safiyar Juma’a inda suka shiga gidaje 13 suna barin wuta tare da cin karensu babu babbaka.

“Da sanyin safiyar Juma’a suka shigo Unugwar Gimbiya da ke Sabo a Karamar Hukumar Chikun, suka kashe mutum biyu suka kuma sace wasu 50,” inji wani ganau.

Wani dan unguwar mai suna Gideon Jatau ya ce ba su taba ganin tashin hankali kamar haka ba.

Ya ce, “Akan yi garkuwa da mutane jefi-jefi amma dai ba a taba yin mai muni irin wannan ba.”

A cewasa, wasu mazauna unguwar sun fara kaura saboda tsoron wani sabon harin.

Aminiya ta tuntubi Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna domin samun karin bayani, amma kakakin rundunar, ASP Muhammad Jalige, ya ce sai ya yi magana da Babban Kwamandan ’Yan Sandan Yankin domin jin abin da ya faru tukuna.

Har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto dai babu cikakken bayani daga hukumomi game da harin.

An samu karuwar hare-haren ’yan bindiga a ’yan makonnin nan a Jihar Kaduna, musamman a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Daga baya dai jami’an tsaro sun fatattake su, inda suka rika bin su har maboyarsu a cikin dazuka suna gamawa da su.