Akalla mutane 17 ’yan bindiga suka kashe, yayin wani hari da suka kai kan kauyen Unguwar Wakili da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.
Da yake ganawa da wakilinmu, Shugaban Kwamitin Tsaro na Masarautar Atyap, Philip Chom, ya ce gawarwakin mutum bakwai aka tsinto a ranar Lahadi baya ga 10 da aka fara ganowa gabanin wannan adadi.
- Buhari ya taya Shugaban China Xi Jinping murnar lashe zabe
- United za ta mayar da Harry Kane mafi tsada a tarihi, PSG za ta gwama Haaland da Mbappe
Philip ya ce gabanin hari, wasu Fulani biyu ’yan kabu-kabu ne suka soma hatsaniya da jami’an tsaro a shingen binciken ababen hawa da ’yan sanda suka kafa a Unguwar Wakili.
Dangane da abin da ya kunno wutar harin, wani mazaunin Zangon Urban mai suna Mukhtar Imran, ya ce wasu Fulani makiyaya biyu – Umar Sambo mai shekara 14 da Sufyan Usman mai shekara 15 – aka soma kashewa a harin.
A baya dai rahotannin da suka fara fita sun bayyana cewa mutane 15 ne suka rasa rayukansu a harin ’yan ta’addan, amma daga baya mutane biyu daga cikin ukun da suka jikkata suka mutu, abinda ya sa adadin mamatan kaiwa 17.
Bayanai daga wasu majiyoyi sun ce akasarin wadanda ‘yan bindigar suka kashe mata ne da kananan yara, cikinsu har da wata mata da jaririnta.
Yayin zanta wa da manema labarai, Shugaban Karamar Hukumar ta Zangon Kataf, Francis Sani ya ce, ‘yan bindigar sun afka wa kauyen na Ungwar Wakili ne da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar.
A cewarsa, nan take ’yan bindigar suka bude wuta kan jama’a, yayin da suka jikkata wasu da wukake, inda suka shafe sa’o’i suna tafka ta’asar.
Tuni dai aka kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kauyen na Unguwan Wakili, da sauran yankunan da ke kusa da suka hada da Mabuhu, Zangon Urban da kuma Unguwan Juju, domin bai wa sojoji damar maido da tsaro a yankunan.