✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 14,500 a shekara 4 A Yankin Sahel–ECOWAS

ECOWAS ta ce mutum miliyan 5.5 kuma sun rasa matsugunnansu a yankin a tsawon lokacin

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta ce akalla mutum 14,500 ne ’yan bindiga suka kashe a yankin a shekaru hudu da rabin da suka shude.

Shugaban ECOWAS mai barin gado, Jean-Claude Kassi Brou, ya bayyana cewa mutum miliyan 5.5 kuma an raba su da matsugunnansu a tsawon lokacin a yankin.

Brou ya bayyana cewa, “Tabarbarewar tsaro ta haifar da matsala ba kawai ga yankin Sahel ba — wanda ya hada da Mali da Burkina Faso Nijar da kuma Arewa maso Gabashin Najeriya —, har da Côte d’Ivoire da Jamhuriyar Benin da kuma Togo.

“Hare-haren ’yan ta’adda da na ’yan fashin daji sun jefa wadannan kasashe cikin halin makoki inda suka hallaka mutum 14,500 a shekara hudu da rabi da suka gabata.

“Hakan kuma barazana ce ga zaman lafiyar al’ummomin karkara da kuma tilasta wa jama’a yin hijira domin neman mafaka a wasu wurare.”

Brou ya bayyana hakan ne a wajen bikin mika ragamar mulki ga sabon shugaban ECOWAS, Dokta Omar Alieu Touray.

Ya ci gaba da cewa, kungiyar ta yi bakin kokarinta wajen tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa da abubuwan bukata don su samu sauki.

Don haka ya yi kira ga kasashen kungiyar da su ci gaba da zama a dunkule kana su bai wa sabon shugabancin kungiyar goyon bayan da ya dace.

A nasa jawabin, sabon shugaban na ECOWAS, Touray, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar da su ci gaba da mara mata baya ta hanyar biyan haraji da sauransu.

Baya ga alwashin yin aiki tukuru da ya yi don ci gaban kungiyar, Touray ya yaba wa Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari kan rawar da yake takawa don ci gabanta.