Dandazon wasu ’yan bindiga sun kashe mutum 10 tare da sace wasu 45 da daruruwan shanu a Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato.
Mahara kimanin 100 ne suka yi aika-aikan a wasu kauyuka uku cikin kwana biyu, inda a ranar Litinin suka sace shanu 200 a garken dabbobin da ake kaiwa Kasauwar Illela.
- An kama mai shekara 70 kan luwadi da yaro mai shekara 12
- Masu yada labaran karya a Intanet za su gamu da azabar Allah – Umar Sani Fagge
Daga nan suka je kauyen Damba da ke yankin Gigane suka yi garkuwa da mutum 45 mata da maza da kananan yara.
Majiyarmu ta ce, “A jiya (Talata) bayan Sallar magariba suka shigo garinmu Buwadai, mutanenmu sun yi kokarin kare kansu sosai, a nan ne aka kashe mutum 10.
“’Yan bindigar ba sa kan abin hawa, a kasa suke tafiya, amma suna da yawa, za su kai 100, a haka suka ci karensu babu babbaka suka wuce”.
’Yan bindiga sun addabi yankin Illela
Mahara sun addabi yankin Gwadabawa da Illela a kwanan nan inda suke ta kai hari, inda ko a satin nan sun yi garkuwa da mutum 16 a garin Gwadabawa, wadanda har zuwa hada wannan rahoto ba a sake su ba.
Shugaban Karamar Hukumar Illela, Injiniya Aliyu Salihu, ya ziyarci kauyen na Buwade domin ganin barnar da ’yan bindigar suka yi tare da jajantawa kan rasa maza 10 da aka yi da duba wadanda aka yi wa rauni da bayar da hakuri ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.
Shugaban ya yi addu’ar samun zaman lafiya a yanki da ganin an sake daukar mataki domin kawo karshen matsalar a yankin.
A bangare guda kuma, Shugaban Kwalejin Kiyon Lafiya ta Gwadabawa, Alhaji Nasiru Gwadabawa, ya karyata jita-jitar da ke cewa ’yan bindiga sun yi kokarin kai wa makaratar hari har k sau uku ba tare da nasara ba.
Shugaban ya ce labarin karya ne aka yadawa da kokarin samar da tashin hankali a cikin al’umma ba wani abu mai kama da wannan.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar, bai daga kiran da aka yi masa domin sanin matakan da ake dauka ba a yankin.