✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 5 a Neja

'Yan bindigar sun kai hari wasu gidaje uku, inda suka kashe mutum daya suka garkuwa da biyar.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum daya tare da sace wasu biyar a garin Bwari- Sabo da ke Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja.

Aminiya ta gano cewa garin ya hada iyaka da Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wani mazaunin yankin mai suna Shu’aibu ya ce ’yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 12 na dare, inda suka harbe wani mutum da ya yi yunkurin tserewa yayin da suke harbe-harbe, nan take kuma ya mutu.

A cewarsa, masu garkuwar sun kai hari kan wasu gidaje uku, inda suka kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da mutum biyar zuwa cikin daji.

Shu’aibu ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ya yi kokarin tserewa ta bayan gidansa ba tare da sanin ashe akwai wasu a bayan gidan sun yi kwanton bauna ba.

Ya ce daga baya an garzaya da marigayin zuwa asibiti a yankin inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Shugaban Karamar Hukumar ta Tafa, Ibrahim Mami Ijah, ya tabbatar da faruwar harin, duk da yake bai yi cikakken bayani kan lamarin ba.