✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe matafiya sun sace wasu a Zamfara

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna ’yan bindiga sun kashe matafiya da dama sun sace wasu a kan Babbar Hanyar Funtua-Gusau da ke jihar.

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna ’yan bindiga sun kashe matafiya da dama sun sace wasu a kan Babbar Hanyar Funtua-Gusau da ke jihar.

Tsohon dan Majalisar Wakilai, Kabiru Yahaya, na daga cikin matafiyan da suka samu rauni harin, kamar yadda hadiminsa, Musbahu Aliyu, ya shaida wa kafar Premium Times.

Musbahu wanda ya ce an garzaya da tsohon dan majalisar asibiti a Gusau, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun kai harin ne a tsakanin Kucheri–Magazu da ke Karamar Hukumar Tsafe da yammacin ranar Laraba.

Ya kara da cewa “Sai da suka jira lokacin isowar motoci daga Gusau, inda suka rika harbi babu bakkautawa, wanda ya sa hanya ta toshe.”

Musbahu wanda ya ce an garzaya da wadanda harin ya shafa Babban Asibitin Tsafe, amma “ba a tantance adadin wadanda aka yi garkuwa da su ba. Sun yi awon gaba da daukacin fasinjojin motocin.”