✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jariri sun kuma sace dan KASTELEA

A makon jiya ne wadansu ’yan ta’adda a yankin Birnin Gwari suka harbe wani jariri ya mutu nan take sannan suka sace wani Ma’aikacin Kula…

A makon jiya ne wadansu ’yan ta’adda a yankin Birnin Gwari suka harbe wani jariri ya mutu nan take sannan suka sace wani Ma’aikacin Kula da Ababen Hawa na Jihar Kaduna (KASTELEA) a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Ma’aikacin KASTELEA din mai suna Hamza yana hanyarsa ce ta komawa gida Birnin Gwari inda iyalansa suke lokacin da wannan lamarin ya faru.

Wani dan sintirin da ke yankin wanda kuma bai so a ambaci sunansa saboda tsaro ya tabbatar wa Aminiya cewa motoci biyu aka kai wa hari a ranar kuma daya daga cikin direbobin motar ya rasa ransa.

“Eh, motoci biyu aka kai wa hari a ranar a wani wuri da ake kira Gaban Gayan ’yan kilomita kadan daga Kuriga a kan titin Kaduna zuwa Birnin Gwari. ’Yan ta’addan sun bude wa motocin wuta ne har harshashi ya samu jaririn da ke hannun mahaifiyarsa da ke cikin daya daga cikin motocin biyu.

Nan take mutum daya ya rasu sannan wanda muke tsammanin direban motar ne. Mutum biyu sun samu raunuka an kuma kwashe su zuwa wani asibiti da ke Kaduna. An yi jana’zar jaririn domin wanda shi da mahaifiyarsa ’yan wani kauye ne da ke kusa da Kuriga, “ inji shi.

A cewarsa mahaifiyar yaron ma ta samu rauni amma babu cikekken bayani a kan ko suna cikin motar da aka sace dan KASTELEA ne a lokacin hari da aka kai musu.

Domin samun tabbacin lamarin, Aminiya ta tuntubi wani jami’in KASTELEA a Kaduna wanda ya bukci a boye sunansa, inda ya tabbatar da sace abokin aikin nasu.

Ya ce  sun sace shi ne a kan hanyarsa ta zuwa hutun karshen mako a gida kuma sun kira cewa suna bukatar kudin fansa. Sannan ya bayyana abokin aikin nasu a matsayin mutumin kirki.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya ce zai kira wakilinmu idan ya samu cikakken bayanin abin da ya faru amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada labarin.