’Yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar ’Yan Sintiri ta Jihar Kaduna (KADVIS) uku a Karamar Hukumar Chikun ta jihar.
An bindige jami’an ne a kauyen Dende a hanyarsu ta dawowa daga Damba-Kasaya da ke Buruku.
- #EndSARS: Buratai ya yi fatali da rahoton CNN
- Mahara sun kashe mutum 11 a Kaduna
- An kashe hakimi da dansa a Kudancin Kaduna
- Sace mata 26: Tattaunawa kai tsaye da Bulama Bukarti
“Suna dawowa ne unguwar lokacin da aka kai musu hari aka kashe mutum uku daga cikinsu”, inji Mista Luka Barde, mazaunin unguwar.
Ya tabbatar wa wakilin Aminiya cewa lamarin ya auku ne a daren Laraba.
Kwamishinan TSaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Ya ce mamatan su hada da Alison Musa, Dauda Audu da kuma Ishaya Sarki, akwai kuma Ayuba Tanko Doza Adamu da ke kabar magani sakamakon raunukan da suka samu.