✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe DPO a Zamfara

Wasu ’yan bindiga sun harbe DPO na garin Maru a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, SP Kazeem Raheem.

Wasu ’yan bindiga sun harbe DPO na garin Maru a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, SP Kazeem Raheem.

’Yan bindigar sun kashe shi ne tare da wani dan sanda mai mukamin Sajan da wani dan banga a lokacin da suka kai dauki domin ceto wani dan kasuwa da ’yan bindiga suke kokarin yin garkuwa da shi.

Wani mazaunin garin Maru ya ce jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a musayar wuta bayan ’yan bindiga sun yi kokarin sace wani dan kasuwa wanda da farko suka sace da dan uwansa, amma suka sako shi bayan an biya kudin fansa.

Daga baya sun sake zuwa za su dauke shi, amma ya tsere, shi ne suka tafi da matarsa.

Ya ce SP Kazeem Raheem ya jagoranci jami’ansa domin kubutar da dan kasuwar, amma suka rasa rayukansu.

“Abin tashin hankali ne kwarai, na tashi da jin karar harbi babu kakkautawa da misalin karfe 2 na dare.

“’Yan bindiga suna yawan kawo hari a garin Maru kuma sun sace mutane da yawa a cikin shekara guda da ta gabata,” in ji shi.

Kokarin wakilinmu na ji daga bakin kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ci tura, saboda bai amsa waya ba, har zuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan rahoton.

’Yan ta’adda na yawan kai hare-hare a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya duk da kokarin jami’an tsaro na ganin bayansu.