✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe direba sun sace fasinjoji 13 a Nasarawa

Masu garkuwa da mutane sun harbe wani direba tare da sace fasinjoji 13 a kan hanyar da ta tashi daga Shafa zuwa Abakpa ta dangana…

Masu garkuwa da mutane sun harbe wani direba tare da sace fasinjoji 13 a kan hanyar da ta tashi daga Shafa zuwa Abakpa ta dangana da Umaisha a Karamar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa.

’Yan bindigar sun harbi marigayin sau uku a ciki kuma ya rasu ne a daren Talata, a Ssibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda wani direban da aka harba yake karbar magani.

Wani direba, wanda ya tsallake rijiya da baya daga harin, Ibrahim Saidu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na Yammacin Talata lokacin da masu garkuwar dauke da bindigogin AK-47 suka fito daga daji suka yi wa wasu motoci da ke zuwa kauyen Ugya kwanto.

Ya ce masu satar mutanen, sun bude wa motocin fasinjar wuta ne a wani mummunan kwana, inda daya daga cikin direbobin ya mutu, dayan direban ya samu raunin harbi.

Ya ce nan take masu garkuwar suka kewaye motocin bayan direban ya rasa yadda zai yi da motar da ta shiga daji; suka yi awon gaba da fasinjoji 13 ciki har da wata mata matashiya.

“A gaskiya, ina tuki a bayan motoci hudu da ke gabana, amma Allah ne Ya cece ni, lokacin da na tsaya a wani kauyen don in dauki fasinja. A daidai lokacin da nake tahowa na ji karar harbe-harbe kuma nan da nan na juya,” inji shi.

“Akwai wasu ragowar wadannan ‘yan fashi da har yanzu suke addabar mutanenmu a wannan hanyar, wanda nake kira ga gwamnatin jihar da ta hada kai da gwamnatin tarayya don ganin an fatattaki ragowar wadannan ’yan ta’addan gaba daya,” in ji shi.

Kusan mako biyu da suka gabata, masu satar mutane sun sace matafiya tara da ke dawowa daga kasuwar Ugya ta hanyar, inda aka ce an biya Naira miliyan 9 a matsayin kudin fansa kafin su samu ’yancinsu.

Lokacin da aka tuntubi kakakin  ’yan sandan Jihar ta Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce ba shi masanaiya kan lamarin; amma zai sanar da baturen ’yan sanda na shiyyar Toto don samun cikakken bayani game da lamarin.