✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe Basarake a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Dakacin garin Kujemi, da ke gundumar Dansadau a Karamar Hukumar Maru a jihar, lokacin da ‘yan…

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Dakacin garin Kujemi, da ke gundumar Dansadau a Karamar Hukumar Maru a jihar, lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari cikin garin.

A ranar Litinin ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu, ya sanar da hakan sannan suka kashe wani mutum guda bayan kashe Dakacin.

SP Mohammad, ya ce an kashe Dakacin ne lokacin da ya kai ziyara garin Kauraci, duk a cikin gundumar Dansadau.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin ne kan babura da misalin karfe 8:40 na dare ranar Lahadi, inda suka yi ta harbin duk wanda suka samu.

Rahoton na cewa, an kashe  wani mazaunin garin Karauchi, mai suna Mustapha Halilu, lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.