✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe basarake a Kaduna

Maharan sun zo da zummar su kashe shi, ba don karbar komai daga gare shi ba.

Ana zargin wasu ‘yan bindiga sun kashe Alhaji Musa Abubakar, Mai Garin Kauyen Runji na Gundumar Auchan a Karamar Hukumar Ikara ta jihar Kaduna.

An kashe Mai Garin ne bayan da maharan suka afka gidansa da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Dan marigayin, Suleiman Musa, wanda kuma shi ne Mai Garin kauyen Rafin Rogo, ya tabbatar da lamarin yayin zanta wa da Aminiya, inda ya ce maharan sun harbi mahaifin nasa har sau hudu.

A cewar Suleiman Musa, “da misalin karfe 2.00 na dare suka shigo gidan bayan sun hauro ta katanga, kuma suka kashe shi da misalin karfe biyu da rabi.”

“Maharan sun zo da zummar su kashe shi, ba don karbar komai daga gare shi ba, saboda ya ba su kudi, sun ki, ya ba su motarsa, suka ki, suka ce, an aiko su ne su kashe shi, in ji shi.”

Haka zalika Shugaban Karamar Hukumar Ikara, Alhaji Salisu Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka aika da jami’an tsaro kauyen na Runji tare da tabbatar da cewa za a gano wadanda suke da hannu a kisan mai garin kuma a hukunta su.

An yi jana’izar mamacin da safiyar yau ta Lahadi kamar yadda koyarwar addinin musulunci ta tanada.