✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje farmaki a hanyar Zamfara

Wata majiya ta ce an harbi mutum uku amma babu wanda ya mutu.

Wasu mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a kan hanyarsu ta komawa Kano daga Jihar Zamfara.

An bayyana cewar harin wanda ya auku a ranar Laraba ya raunata akalla ’yan sanda uku daga cikin ayarin gwamnan.

  1. Kasashen da Nnamdi Kanu ya je kafin a kama shi
  2. Za a rataye ’yan bindiga da masu satar mutane a Neja

Majiyarmu ta ruwaito cewa Gwamna Ganduje ba ya cikin ayarin, kasancewar yana cikin tawagar Gwamnan Jihar Jigawa wanda tuni ayarinsu ya yi nisa a lokacin da lamarin ya faru.

Bayanai sun ce Gwamna Ganduje yana cikin tawagar Gwamna Abubakar Badaru, da suka baro Zamfara bayan halartar taron sauya sheka da Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar, sai dai an yi rashin sa’a dukkan wayoyinsa a kashe suke a lokacin hada wannan rahoto.