’Yan bindiga sun kai hari tare da tarwatsa mazauna ƙauyuka biyar da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sonudazuwa, Tsauni Dodo, da Dandauka.
- Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai
- Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo
Wani jagoran al’umma ya tabbatar da faruwar harin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki sansanin Fulani da ke Kubuwo, inda suka sace matasan makiyaya uku.
Sun kai harin ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 6 na yamma.
Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar sun isa ƙauyukan suna harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.
“’Yan bindigar sun shigo suna harbi ta ko ina. Mutane suka riƙa gudu don tsira da rayukansu,” in ji wani jagora.
“Sannan sun sace matasa uku a sansanin Fulani, suka tafi da su cikin daji.”
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa ’yan bindigar sun tserewa wani farmaki da sojoji suka kai musu a dajin Kurutu-Azara, wanda ke iyaka da Ƙaramar Hukumar Kagarko.
Ya ce a kan hanyarsu ta tserewa ne, suka farmaki ƙauyukan da ke hanyarsu.
A yayin harin, ’yan bindigar sun ƙone mota da babur a Unguwan Tauka.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, “An ƙone wa wani mutum mota sabuwa da ya sayo a Kaduna. Yana kan hanyar shigowa garin ne sai ya hango ’yan bindigar.
“Nan take ya fice daga motar ya tsere, suna ganin motar suma cinna mata wuta suka ƙone motar da wani babur.”
Wani ɗan banga daga cikin ƙauyukan da aka kai wa harin ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da bin sahun ’yan bindigar.
Rundunar ’yan sandan yankin ta tabbatar da harin, amma ta ce za a tuntuɓi hedikwatar ’yan sandan m Kaduna don ƙarin bayani.
Sai dai kakakin rundunar, ASP Hassan Mansur, bai samu damar yin tsokaci kan harin ba lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.