✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

’Yan bindiga sun kai hari Tegina  

Rahotanni da a halin yanzu ke fitowa daga garin Tegina na Karamar Hukumar Rafin Jihar Neja, sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun yi garin…

Rahotanni da a halin yanzu ke fitowa daga garin Tegina na Karamar Hukumar Rafin Jihar Neja, sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun yi garin kawanya suna cin karensu babu babbaka.

Majiyoyi daga garin sun ce a halin da ake ciki ’yan bindigar sun fantsama a cikin babban garin Tegina inda suke harbi kan mai tsautsayi.

A cewar wata majiyar jami’an tsaro a yankin, kowa na ta kansa inda jama’a ke buya domin tsirar da rayukansu.

“’Yan bindiga suna nan a cikin garin Tegina a halin yanzu. Garin na cikin yanayi na fuskantar hari a yanzu.

“Ina cikin mabuya a yanzu da nake magana, don Allah ku yi mana addu’a, don Allah,” inji majiyar.

Wasu majiyoyin su ma sun tabbatar da cewa garin na Tegina a halin yanzu ’yan bindiga sun mamaye garin kuma sun datse hanyar Tegina-Zungeru-Minna inda suke tare masu ababen hawa.

Sai dai ko da wakilinmu a ya tuntubi kakakkin rundunar ’yan sandan DSP Wasiu Abiodun bai iya samun shi a wayar tarho ba domin jin ta bakinsa.