✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari ofishin ’yan sanda, sun sace uwa da ’yarta

Maharan dai na kokarin sace magidanci ne, amma suka ɗauke matarsa da ’yarsu.

Wasu mahara da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari ofishin ’yan sanda da ke Ngurore a Karamar Hukumar Yola ta Kudu sannan suka sace wata uwa mai shayarwa.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Sulaiman Nguroje ne ya tabbatar da kai harin ga manema labarai ranar Lahadi.

A cewarsa, an kai harin ne da misalin karfe biyu na dare, ko da yake ya ce ba a sami asarar rai ko daya ba.

“Masu garkuwar suna hankoron kama wani Alhaji Umaru ne mazaunin garin Ngurore a Karamar Hukumar Yola ta Kudu.

“Sun raba kansu gida biyu ne; kaso daya suka kai hari ofishin ’yan sandan, domin su dauke hankalinsu, yayin da ragowar kuma suka kai hari gidan nasa, inda suka yi awon gaba da matarsa, Hauwa Umaru da ’yarta.

“Tuni Kwamishinan ’yan sanda, Mohammed Barde ya bada umarnin a aike da jami’ai masu yaki da satar mutane don ceto su,” inji shi.

Nguroje ya ce  ana sa ran jami’an su gudanar da sintiri na musamman a wuraren da aka tabbatar bata-garin na amfani da su a matsayin maboya don ceto wadanda aka sace din tare da kama masu garkuwar.

Kakakin ya ce tuni jami’an da ke karkashin jagorancin SP Babagana Abubakar suka bazama kokarin ceto mutanen.