Wasu ‘yan bindiga da ake zargin an turo su ne, sun kai hari gidan Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha mai barin gado da ke unguwar Ogboko, a karamar hukumar Ideato ta Kudu ta jihar Imo, ranar Juma’a da daddare.
‘Yan bindigar sun shiga gidan Gwamnan ne da misalin karfe 2:00 na tsakar dare inda suka yi nasarar fin karfin jami’an tsaron gidan har suka shiga harabar gidan.
Wata majiya daga iyakan Rochas sun ce, ‘yan bindigar ba su dauki komai a gidan ba. Sai dai ana zargin an turo su gidan Gwamna da wata manufa.