’Yan bindiga sun harbe Shugaba Jovenel Moise na kasar Haiti, yayin wani hari da suka kai gidansa da ke Port-au-Prince, babban birnin kasar.
Firaiministan rikon kwaryar kasar, Claude Joseph ke sanar da labarain kisan gillar da ya auku da misalin karfe 1 na daren Laraba.
Wata sanarwa da ofishin firaiministan ta fitar, ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta nemi jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Sanarwar ta ce an dauki dukkan matakan da suka dace na ci gaba da tafiyar da kasar a yayin da ikon tsaro yana hannun soji da jami’an ’yan sanda.
Kafar watsa labarai ta France24 ta ruwaito cewa, ’yan bindigar da ba a kai ga gano ko su waye ba, sun kai hari gidan Shugaba Moise inda suka yi masa ruwan harsashi.
Bayanai sun ce yanzu haka Uwargidan shugaban tana kwance a Asibiti sakamakon raunuka na harsashi da ta samu.
Tun a shekarar 2018 Moise yake mulkar kasar wacce aka kiyasta cewa ita ce mafi talauci a nahiyyar Amurka.
Baya ga dambarwar siyasa, sace-sacen mutane don neman kudin fansa sun kara ta’azzara cikin watannin baya bayan nan, lamarin da ya kara nuna tasirin tsageru masu dauke da makamai a kasar da ke yankin na Carribean.
Kazalika, kasar tana fuskantar matsanancin talauci gami da aukuwar bala’o’i irinsu girgizar kasa da makamantansu.