Shugabannin kasashen duniya sun aike da sakon ta’aziyya tare da yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Shugaban Kasar Haiti Mista Jovenel Moïse.
Firayi Ministan Birtaniya, Mista Boris Johnson ya fadi a shafinsa na tiwita cewa yana bakin ciki kan kashe Mista Moise, inda ya kira hakan da mummunan abin kyama.
Shugaban Amurka Mista Joe Biden ma ya mika ta’aziyya ga mutanen Hiati kan abin da ya kira “kisan gilla mai ban tsoro.”
Wadansu ’yan bindiga ne suka harbe Shugaba Jovenel Moïse a gidansa inda suka raunata matarsa a asubahin shekaranjiya Laraba.
Firayi Ministan Kasar Mista Claude Joseph ne ya tabbatar da kashe Shugaban inda ya ce ’yan sanda da sojoji suna kula da tsaron kasar, wadda take fama da rashin tabbas a fagen siyasa da neman kafa mulkin dimokuradiyya.
Titunan Port-au-Prince, babban birnin kasar sun kasance fayau, a Larabar makon jiya, yayin da wadansu mutane suka rika fasa shaguna a wani yanki.
Mahukuntan kasar sun kafa dokar ta-baci a kasar tare da rufe filin jirgin saman birnin a daidai lokacin da ake tsoron ta fada a cikin rikici a yayin da ake tunkarar babban zaben kasar a wani lokaci a bana.
Marigayi Shugaba Moise mai shekara 53, yana mulkin kasar ce a karkashin dokar soji a sama da shekara guda bayan da kasar ta gaza gudanar da zabe.
Kuma mutuwarsa ta zo a daidai lokacin da ’yan adawa suka rika neman ya sauka daga mulki a ’yan watannin nan.
Rikicin siyasa ya raba mutum dubu 14 da 700 da muhallinsu a kasar ta Haiti.
Tsohon Shugaban Kasar Mista Michel Martelly, wanda Mista Moise ya gada ya ce yana addu’ar samun lafiya ga Uwargidan Shugaban Kasar Misis Martine Moïse, inda ya bayyana kisan da “babbar koma-baya ga kasar da dimokuradiyyar Haiti.”
Misis Martine Moïse mai shekara 47, an harbe ta a yayin harin kuma an kai ta asibiti.