✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun hallaka mutum 10 a Katsina

Mahara sun kashe jami'in kwastam da wasu mutum a Jihar Katsina a ranar Juma'a

Wasu da ake kyautata ‘yan bindiga ne sun kashe hafsan hukumar Kwastam a kauyen Dan Arau da ke kan hanyar Katsina zuwa Jibiyaa Jihar Katsina.

Maharan sun kuma hallaka mutum tara a kauyen Tsauwa na Karamar Hukumar Batsari a ranar Juma’a.

“Gaskiya ne ’yan bindiga sun hallaka jami’in kwastam a wani wurin binciken ababen hawa a kauyen Dan Arau, amma in kuna son karin bayani sai dai ku tuntubi hukumar ta hana fasa kwauri”, inji Kakakin Rundunar ’yan sana na jihar Katsina Gambo Isa.

Rahotanni sun ce maharan sun kashe mataimakin sufuritanda kwastam din mai suna Garba Nasiru, ne a harin da suka kai a ranar Juma’a.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa sai da jami’an tsaro suka yi ta musayar wuta kafin su kwato gawar mamacin daga hannun maharan.

An kuma yi jana’izar jami’in tsaron tun a ranar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

A harin Batsari kuwa da ya yi sanadiyyar rasuwar mutum tara, rahotanni ce ’yan bindigar sun yi wa kauyen kawanya suka kuma saci babur din hawa da sauran abubuwa kafin su tsere.

Tun da farko an tabbatar da cewa sun hallaka mutum tara kafin daga bisani kuma su fantsama a cikin daji.