’Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja sun harbi daya daga cikin fasinjoijn da suka rage a hannunsu.
Daya daga cikin masu shiga tsakani domin a sako fasinjojin, Malam Tukur Mamu, wanda ya sa baki aka sako 11 daga cikin fasinjojin, ya ce mutumin da aka harba din yana cikin mawuyacin hali bayan harbin da suka yi mishi.
- ’Yan Bindiga sun kwace kauyuka 30 a Zamfara —Gumi
- Babu gudu ba ja da baya kan daukar bindiga don kare kai a Zamfara —Matawalle
“Kashe mutanen da ke hannunsu abu ne da muka san za su iya tunda a baya sun yi barazanar aikatawa,” inji shi.
Ya bayyana cewa gwamnati na tattaunawa da maharan a-kai-a-kai, amma har yanzu ba ta yi wani kwakkwaran motsi ba.
“Na san abin da ke cikin wannan matsala shi ya sana nake nanata cewa ya kamata Shugaba Buhari ya dauki wasu matakai, marasa dadi, matukar za su kai ga kubutar da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”
“Da abin da muka samu nasarar yi na bude kofar, gwamnati na da karfin ikon kawo karshen wannan lamari a cikin ’yan kwanaki.
Shugaba Buhari dai ya sha ba wa jami’an tsaro umarni cewa su kabutar da fasinjojin jirgin kasan ba tare da komai ya same su ba.