Da safiyar ranar Talata ce wasu ’yan bindiga suka kai hari Karamar Hukumar Amaekpu Ohafita da ke Jihar Abiya inda suka kone ofishin Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).
Kwamandan Hukumar a Jihar, Mista Akingbade Bamidele ne ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin, sai dai ya ce an yi sa’a babu rai ko daya da ya salwanta.
- Sallah: An baza jami’an KAROTA 1,000 a kan titunan Kano
- Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari karamar hukumar inda suka kone ofishin ’Yan sanda da na Hukumar Zabe ta kasa (INEC).
An yi ta kai hare-hare kan jami’an tsaro da kayayyakin more rayuwa a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin kasar a makonnin da suka gabata, inda rayukan jami’an tsaro da dama salwanta da lalata ofisoshin ’yan sanda.
Ana zargin haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara (IPOB) da alhakin wannan hare-hare da suka addabi Kudancin kasar.